An Tuhumi Dan Sandan Da Ya Harbe Bakar Fata Da Laifin Kisan Kai

An tuhumi dan sandan jihar Texas da ya harbe wata mata baƙar fata har lahira a gidanta da laifin kisan kai.

An kama Aaron Dean 'yan sa'o'i kadan bayan da ya yi murabus daga rundunar yan sanda ta Fort Worth jiya Litinin.

Shugaban ‘yan sanda na birnin, Edwin Kraus, ya fada a wani taron manema labarai cewa, da za a kori Dean din idan har bai yi murabus ba.

Dean, wanda farar fata ne, ya harbe Atatiana Jefferson,bakar fata 'yar shekaru 28 da haihuwa. ta tagar gidanta a ranar Asabar bayan da wani makwabcinta ya kira lambar 'yan sanda wanda ba na neman agajin gaggawa ban, don sanar musu cewa an bar kofar gidan Jefferson a buɗe.