Abuja: Gangamin Kungiyoyin Mata a Birnin Tarayya

Gangamin kungiyoyin mata a Abuja

Wata hadakar kungiyar mata ta gudanar da gangami a birnin tarayya Abuja na Najeriya, da nufin hada kan ‘yan siyasa da magidanta da matasa da kuma mata, kan illar bangar siyasa da kuma tada hankali lokacin da kuma bayan zabe.

A cikin jawabinta, babbar mai jawabi a gangamin wadda kuma take wakiliyar cibiyar mata ta MDD a Najeriya, wadda kuma take wakiltar cibiyar a kungiyar ECOWAS Comfort Lamtey, ta ce yin wannan gangamin ya zama wajibi kasancewa mata da kananan yara ne suke tagayyara idan aka fuskanci tashin hankali.

Shugabannin kungiyoyin mata da suka gabatar da jawabai a wajen ganganin sun bayyana cewa, taron bashi da alaka da wata jam’iyar siyasa, ko kungiyar addini dalili ke nan da mata suka yi dafifi zuwa zangon taron da aka gudanar a Unity Fountain dake tsakiyar birnin tarayyar.

Gangamin kungiyoyin mata a Abuja

Matan da suka hallarci gangamin sun fito daga dukkan jihohin tarayyar Najeriya, suka kuma jaddada cewa ba za su lamunci amfani da su ko ‘ya’yansu wajen biyan bukatar wani dan siyasa a wannan zaben ba.

Domin Karin bayani saurari rahotan Alheri Grace Abdu.

Your browser doesn’t support HTML5

Abuja: Gangamin Kungiyoyin Mata a Birnin Tarayya - 3'27"