Adamawa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Shugabannin Kungiyoyin Fulani

Kamar yadda rahotanni da al’ummomin yankin dake kan iyakar Najeriya da Kamaru suka tabbatar, wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da jama’a ne, suka dauke wasu manoma da kuma wasu dake kula da dabbobinsu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce tuni aka baza komar farautar 'yan bindigan da suka sace wadannan mutane.

Wannan matsala ta sace mutane domin neman kudin fansa, yanzu haka na neman gagarar kundila a Najeriya, al'amarin da yasa hukumomin tsaro hada kai, da shugabannin kungiyoyin sakai ciki har da na Fulani makiyaya irinsu Miyetti Allah da Tabital Puulaku.

To sai dai kuma, ya yin da wasu ke taimakawa yanzu haka 'yan bindigar sun fara bin wasu shugabanin kungiyoyin Fulanin har gida suna kashewa, kamar wanda ya faru cikin kwanakin nan, inda aka kashe wani fitaccen shugaban kungiyar Tabital Puulaku, na jihar Adamawa, Abdu Bali.

Muhammad Jika Buba, kakakin kungiyar Miyetti Allah a jihar Adamawa, ya ce duk da kisan da ake yiwa shugabanin, babu wani kulawa da iyalan wadanda aka kashen ke samu daga hukumomi, batun da ya ce yanzu jikinsu ya yi sanyi.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindigan Sun Fara Bin Shugabannin Kungiyoyin Fulanin Suna Kashewa