Aiwatar Da Shirin "Ruga" Na Iya Rage Matsalar Tsaro: Miyetti Allah

Makiyayi dan kungiyar Miyetti Allah

Fulani sun nemi a gwada shirin da gwamnatin kasar ta fito dashi a shekarar 2019 na “Ruga” da suke gani mai yiwuwa ya taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta na rashin tsaro.

Wannan kiran ya biyo bayan kaurin suna da kabilar Fulani tayi a Najeriya, da kuma zargin da ake mata na hannu a ayukkan ta'addanci,

Tarihi ya nuna cewa, gwamnatoci da dama lokutan baya, bayan samun ‘yancin kan Najeriya ,sun dauki matakin shawo kan matsalar karancin wuraren kiwo da shayar da dabbobi ta wajen fitarwa Fulani ruggage, burtulla, hurumma da mashayar dabbobi, abinda yasa suke gudanar da harkokinsu na kiwo cikin lumana ba tare da sun sami matsala da manoma ba.

an-kaddamar-da-shirin-ruga-na-farko-a-najeriya

mataimakin-shugaban-najeriya-ya-kaddamar-da-sabon-shirin-ruga-a-adamawa

kungiyar-gwamnoni-arewacin-najeriya-sun-amince-da-shirin-ruga

shirin-tallafawa-dukkan-makiyayan-jihar-kebbi

A cikin hirar su da Muryar Amurka, wadansu masu fada a ji a kungiyar miyetti Allah ta makiyaya sun bayyana gazawar gwamnati wajen aiwatar da wannan shirin ko kuma daukar matakin shawo kan matsalar rikicin Fulani da makiyaya da ake dangantawa da rashin wuraren kiwon dabbobin.

Dattijon kungiyar miyetti Allah ta makiyaya a Najeriya Muhammadu Dodo Oroji yace “ba karamar kasawa ba ce da sakaci ga gwamnati a wayi gari yanzu duk wadannan abubuwan a rasa su, kuma duk da kudurin aiwatar da shirin ‘Ruga' Wanda kan iya yin tasiri wajen maye gurbin wancan tsarin ya gagara, kuma gashi ana kokawa tare da zargin Fulanin.”

Matsugunin Fulani"Ruga" a Najeriya

Bisa ga cewar dattawan kungiyar, akwai alfano da al’umma za ta samu da an aiwatar da wannan shirin na ‘ruga’ da ya hada da samun Fulani su zauna wuri daya ta yadda za a iya tuntubarsu idan bukata ta tashi, haka kuma zasu sami ilimi da zai taimaka wajen hana su shiga ayyukan ta’addanci domin zasu fahimci yadda ake zaluntarsu a basu manyan bindigogi su aikata ta’addanci amma su tashi da kusan babu komi idan aka kwantata da irin kudin da suke karba wajen neman fansa.

A yanzu da yake a Najeriya ana ta kokarin lalabo hanyoyin kawo karshen matsalolin rashin tsaro, wasu na ganin cewa duk shirin da ake tunanin zai yi tasiri ga biyan wannan bukatar, to yana da kyau a bayar da dama a gwada shi koda za'a yi dace.

Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Aiwatar Da Shirin Ruga Na Iya Rage Matsalar Tsaro: Miyetti Allah-3:00"