Akalla Mutane Biyar Sun Halaka A Taraba A wani Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya

TARABA: 'Yan gudun hijira a Taraba

Wani sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Sardauna a jahar Taraba, ya halaka mutane.

Lamarin ya auku ne ranar Alhamis kamar yadda wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko mana da rahoto.

Shi dai wannan sabon tashin hankali na harin da aka kaiwa Fulani makiyaya a yankin, na zuwa ne a kasa da watanni goma da mummunan harin da aka kaiwa wasu yankunan Mambillan da ya jawo hasarar rayuka da dama, tare kuma da tilastawa Fulani fiye da dubu goma sha bakwai gudun hijira.

Kamar yadda ganau suka tabbatar, an samu hasarar rayuka fiye da goma baya ga wadanda aka raunata.

Shiko da yake Karin haske, Hon.Hamidu Ismaila Karkara, kansila mai wakiltan yankin da lamarin ya faru, ya danganta tashin hankalin da rikicin fili da aka dade ana jayayya akai.

Kawo yanzu tuni aka kara tura jami’an tsaro zuwa yankin inda kakakin rundunan yan sandan jihar ASP David Misal ke cewa komi ya fara daidaita a yankin.

Ya kara da cewa bisa kididdigar da suka yi mutane akalla biyar ne suka hakala, sakamakon wannan rikici.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Rikicin Manoma Da Makiyaya A Taraba