Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kaiwa Ma'aikatan Jinkai Hari


Ma'aikatan Jinkai
Ma'aikatan Jinkai

Hukumar kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya, tace wasu ‘yan kungiyar Boko Haram dauke da makamai sun kai hari a kan sojoji a Arewa maso Gabashin Najeriya, inda suka kashe kuma ya raunata ma’aikatan jinkai da yan sanda, inji rahoton wakilyar Muryar Amurka a Geveva Lisa Schlein.

Hukumar tace ana gudanar da bincike a kan harin. Tace abin da ka agano a yanzu shine, mayakan Boko Haram masu yawa, dauke da makamai da bindigogi masu sarrafa kansu da rokoki da gurneti sun kai hari a kan sojoji.

Mai magana da yawun hukumar kula da bakin hauren ta kasa da kasa Joel Millman, yace, ya san cewa akwai sansanin yan gudun hijira na cikin gida a wurin. Millman yace ma’aikatan hukumar bakin hauren dake aiki a sansanin sun ce an kashe sojoji hudu, da yan sanda hudu da kuma ma’aikatan jinkai uku, yayin da wasu a’aikatan guda uku ke fama da rauni kuma mutum guda a cikinsu ya bata.

Joel Millman yace kwai bayani da na samu daga Mohammed Abdiker, darektan ayyuka da jinkai na hukumar, yana cewar, muna bakin ciki da alhinin na kashe abokan aikinmu guda biyu a cikin wani hari da yan Boko Haram suka kai a Arewa maso gabshin Najeriya da yammacin Alhamis. Yace Ibrahim Lawan da Yawe Emmanuel sun taka rawan gani wurin taimakawa fararen hula da yan gudun hijiran cikin gida. Yace zamu kewarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG