Akwai Bukatar Yaki Da Matsalar ‘Yan Ciranin A Nahiyar Afrika

Taron 'Yan Jaridar Nijar

Reshen kungiyar Institut Panos a Afirka ta yamma, da hadin gwiwar UNESCO da AEC, da hukumar kare hakkin bil adama ta kasa CNDH ne suka shirya wani taro da nufin karawa juna sani a tsakanin ‘yan jarida, da jami’an fafutika.

A tabakin jakadan kasar Italiya Marco Principe, matasa ne wadanda suka fi kowa zuwa cirani ta barauniyar hanya da nufin samun rayuwa mai inganci, saboda haka kasar Italiya ta samar da wani shiri na musamman domin ilmantar da matasa illolin dake tattare da irin wannan yunkuri.

Shi kuwa mataimakin magatakardan ministan watsa labarai Sani Abdou, yace samarda kwararan madogara shine matsayin hanya mafi kyau, wajen fitarda tunanin zuwa cirani daga kawunan matasa. Tsarin da ke bukatar gudun mawar kasashe aminan Nijar.

Ana kuma bukatar samar da sahihan labarai a game da zahirin abubuwan dake faruwa da matafiya, da illoli da ke tattare da zuwa ci rani akan iyakokin kasashe cikin shirin wayarda kan al’umma.

Daga shekarar 2016 yawan ‘yan ciranin dake ratsa jamhuriyar Nijar, ya ragu daga 100,000 a shekara zuwa 5,000 sakamakon farautar da gwamnatin kasar ta kaddamar.

Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: An Fara Gudanar Da Taron ‘Yan Jarida Akan Batun Yaki Da ‘Yan Ciranin