Akwai Rade-radin Sabon Hari a Abuja

Jami'an Tsaro a Abuja.

Bayan fitowar rade-radin wani sabon harin, an kara tsaro a babban Birnin Tarayya Abuja yanzu bayan fashewar boma-bomai a tashar motar Nanya da yayi sanadiyar rasa rayuka misalin 75 da jikkata sama da mutane 100 da kuma asarar dukiyoyi Litinin dinnan.
Shaidu sun ce duk ta inda mutun ya fito zai ta ganin jami’an tsaro suna sitiri da kuma bicikar mutane, da kuma masu neman shiga tashar motoci dama majalisar kasar.

Murya Amurka ya sami labarin cewa wadanda suka kai harin Abuja na ikirarin cewa wurare biyar ne mahimmai suke son kai hari a babban birnin taraiya Abuja.

Wakiliyar Muryar Amurka, Madinat Dauda ta bada bayanin cewa “akwai rade-radin cewa wadanda suka kai harin wai sun aika da wasika ga hukumomin Abuja cewa zasu kadamar da wanna harin.”

Your browser doesn’t support HTML5

Tsaro Ya Tsananta a Abuja - 3'30"