Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mene ne Ya Faru a Tashar Nyanya Dake Abuja?


Wadanda harin bom a tashar Nyanya dake Abuja ya shafa, Afrilu 14, 2014.

​Misalin karfe shida agogon Najeriya ne bom ya fashe a tashar motoci dake unguwar Nyanya dake mashigar birnin Abuja ta kudu maso gabas.

Rahotanni sun nuna wani ne ya tuko wata mota dauke da Bom din, ya karata a tashar manyan motocin safa ta El-Rufai, inda ya fice daganan kuma Bom din ya tashi kuma ya hallaka mutane da jami’ai suka ce sun kai 76, sannan wadanda suka ji raunuka sun haura dari.

Abubakar Jos na daya daga cikin mutanen da suka fara isa inda abun ya faru, “walLahi abun ba kyau, gashi da idona na ga gawarwaki.”

Jami’an kashe gobara da na agajin gaggawa da na ‘yan sanda sun kai dauki, inda sukayi jigilar kai gawarwaki asibitocin cikin gari.

Badamasi Nyanya, mazaunin unguwar Nyanya ne, yace “wannan masifar bamu taba ganin irinta ba walLahi, a dai rayuwar mu, walLahi. Duk yadda ake tunanin abun ya wuce nan.”

Hajiya Binta Mu’azu ‘yar Kaduna ce wadda take shiga birnin na Abuja a dai-dai lokacin da abun ya faru.

“Wannan gwamnati, ta duba wannan fitina dake zagaye da mu”, a cewar Hajiya Binta.

Birnin Abuja dai yanzu, bai zama bako da tashin bom ba, idan aka tuna da tashin bom a shedkwatar ‘yan sanda, da kunar bakin wake a ofishin jaridar Thisday, da ofishin Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suka jawo asarar rayuka, da raunata mutane da kuma asarar dukiya.

Bom dai ya fara tashi ne a watan Oktobar 2010 daf da dandalin “Eagles Square”, wanda ‘yan tsageran Niger-Delta suka dauki alhakin danawa.

Ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari na Litinin dinnan.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG