Al'ummomin Arewacin Jihar Nasarawa Sun Bukaci Gwamna Al-Makura Ya Zarce

Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa

Yayin da gwamna Al-Makura ke kiran al'ummomin jihar su hada kai wasu daga arewacin jihar sun saya masa takardar sake tsayawa zabe a shekarar 2015

Gwamnan yayi kiran ne a lokacin da alummar arewacin jihar suka bayyana aniyarsu na cewa gwamnan ya sake tsayawa zabe karo na biyu.

Mutanen arewacin sun saya masa takardar shiga zaben wadda suka mika masa. Gwamnan ya yaba masu ya kuma ce ba zai basu kunya ba.

Gwamna Al-Makura yace mutane ba tare da ya nemesu ba amma sun kirawoshi ya cigaba sabili da haka ba zai basu kunya ba. Ya sake jaddada manufar gwamnatinsa. Yace gwamnati ce da ta kudiri yiwa kowa aiki har da 'yan jam'iyyar PDP domin hakin 'yan jihar ya rataya akansa.

Kokarin da suke yi shi ne yadda zasu taimakawa mutane masu kananan karfi ba tare da la'akari da kabila ko addinin ko jam'iyya ba. Duk dan jihar yana da hakin gwamnati ta taimakeshi. Abin da jihar ke bukata shi ne hadin kan 'yan jihar domin a yi tafiya tare. Tashin hankulan dake faruwa zasu wuce idan duk 'yan jihar suka kuduri aniyar zama lafiya da juna.

Wasu da suka fito daga yankin sun yaba da irin ayyukan da gwamnan yayi masu. Ya basu makarantu da ruwa da hanyoyi abubuwan da suka ce basu gani ba wurin gwamnatocin da suka shude.

Ga rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Al'ummomin Arewacin Jihar Nasarawa Sun Bukaci Gwamna Al-Makura Ya Zarce - 3' 49"