Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa daga Sassan Najeriya Sun ce Lallai APC ta Tsayar da Janaral Buhari a Zaben 2015


Janaral Muhammed Buhari

Yayin da Janaral Muhammed Buhari ke shirin bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugaban kasa yau a Abuja wasu matasa suna ganin ma shi ne ya kamata ya zama dan takarar daya tilo na jam'iyyar APC

Wasu matasa daga bangarori daban daban a Najeriya sun dage cewa Janaral Buhari ne kawai dan takarar da zai iya yin nasara a zaben shekarar 2015.

Alhaji Umar Ibrahim Askon shugaban kungiyar matasa masu goyon bayan Janaral Buhari a jihar Kano yana cikin wadanda suka kirawo taron Kaduna domin tabbatar da goyon baya ga Janaral Buhari. Yace abun da ya sa suke goyon bayan Janaran shi ne suka yadda cewa yana siyasa ne ba domin kansa ba. Shi kadai ne wanda EFCC ta bincika bata sameshi da wani laifin almundahana ba. Yace babu wanda bashi da kashi a gindinsa. Kowane dan takara yana da wani abu a gindinsa da an yi masa barazana sai kauce.

Akan ko APC tana da tabbacin wanda zata tsayar sai Ibrahim Askon yace jam'iyyarsu tana da tabbacin wanda zata tsayar. Yace duk sun fito ne su tallata guda daya.

Dangane da wai Janaran yayi takara sau uku bai samu nasara ba ya kamata ya hakura sai Ibrahim Askon yace wanda yake nema a wurin Allah babu ruwansa da lokutan da ya tsaya zabe. Allah ne yake bayarwa kuma Allah zai bashi.

Shi ma Alhaji Ishak Galadima jagoran kungiyar a jihar Kaduna yace akwai dalilan da suka ga Janaral Buhari ne kawai zai kada gwamnati idan an fita faggen fafata zabe. Kowa ya san ingancin Janaral Buhari da rikon amanarsa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG