Ambaliyar Ruwa Na Baraza A Wasu Jihohin Yankin Niger-Delta

Hukumar bada Agajin gaggawa ta NEMA, ta umurci al’umomin yankunan da ake saran samun amballiyar ruwa su bar garuruwansu saboda gudun kada ambaliyar ta mamaye yankunansu.

Ambaliyar ruwa na dab da mamaye wasu wurare dake kan hanyar ruwa, a wasu jahohi uku dake yankin Naija Delta mai arzikin mai a kudancin Najeriya. Jihohin, a cewar wani rahoto, sun hada da Delta, Edo da kuma Cross Rivers.

Hukumar ta NEMA ta ce garuruwan da lamarin zai shafa a jihar Delta, sun hada da karamar hukumar Ogele ta kudu, da Ogele ta arewa, da kuma karamar hukumar Obimeri.

Al’umomin da su ke zaune a wadannan yankunan, sun fara kokawa akan halin da suke ciki.

Saroni Micheal, ya ce zancen ambaliyar ruwa abu ne da in dai har ya ja zuwa wani lokaci, yakan hana su fita wurin neman abinci da gudanar da sauran al’ammuran yau da kullum musamman a jihar su ta Delta kuma lamarin gaskiya ya kazamta, a cewar Saroni. Ya kuma ce ya kamata gwamnati ta daina korafin cewar mutane ne ke toshe magudanan ruwa saboda lamarin ya baci.

Injiniya Ali Ibrahim, na fanin albarkatun ruwa da kasa, a jami’ar Calabar, ya ce ko a shekarar da ta gabata ta 2018, an yi ambaliyar ruwa har aka sami hasarar rayuka, bayan amfanin gona, da dukiyoyi, da gidajen da suka salwanta.

Shekara da shekaru kwararru a fannin yanayi, sun sha dora laifin wannan matsalar ta ambaliyar ruwa akan rashin ingantattun hanyoyin ruwa.

Mr. Kingsley Nwodibi, shine shugaban wata kungiya ta kare muhalli a yankin Naija Delta. Ya ce zancen toshewar magudanan ruwa a lokacin ruwan sama abu ne wanda idan gwamnati ta so za ta iya kawar da shi nan take saboda magudanan ruwan ana iya yashe su.

Ga karin Bayani a cikin sauti daga Lamido Abubakar Sokoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Ambaliyar Ruwa Na Baraza A Wasu Jihohin Yankin Niger-Delta