Amfanin Goge Bakin Yara Sau Biyu Kowacce Rana

Wasu yara suna goge baki

Hakoran yaran ka zasu iya rubewa idan ba a kula da su ba. Dasashin hakorin yaro bashi da karfi kamar yadda na babban mutum yake – ko sabbin hakoran manya basu da karfi a farin shekarunsu.
Hakoran yaran ka zasu iya rubewa idan ba a kula da su ba. Dasashin hakorin yaro bashi da karfi kamar yadda na babban mutum yake – ko sabbin hakoran manya basu da karfi a farin shekarunsu. Miliyoyin kwayoyin cuta cikin bakin yaron ka zasu iya kawo hatsari a bakin yaronka idan ba’a wanke bakin da kyau ba.

Ciwon hakori zai iya damun cin abinci, barchi da kuma raya ilimi a mahimman lokaci da yara suke girma. Rubewar hakorin kananan yara kuma yana jawo damuwan hakori da zai zauna har idan yara sunyi girma. Hakora marasa pasali babu dadin gani.

Domin kare wadannan damuwar, likitoci sun bada shawarar cewa yara su goge bakinsu akalla sau biyu a yini da man goge baki; na farko da safe da kuma bayan an ci abinci da dare.

Wannan bazai taimaka wanke kwayar cutar ba ne kawai, amma man goge baki yana taimakon karfafa hakokara da kuma kiyaye su daga rubewa.