Accessibility links

Kimanin mutane tamanin da huidu ne suka mutu sandiyar barkewar zazzabin ebola a kasar Guinea .

Jakadan Najeriya a kasar ta Guinea, Babangida Ibrahim shine ya bada wannan bayanin da yake tattaunawa da sashen Hausa.

A cewar Jakada Babangida, shekarun baya a wasu kasashe irin su Zaire da Sudan, an sami bullar wannan zazzabin na ebola.

A dai-dai wannan lokaci da zazzabin Ebola ke daukar rayukan mutane a Guinea da Liberiya, manazarta na kokarin kara fahimtar wannan cuta, da hanyoyin magance ta.

Jakada Babangida Ibrahim yace hukumomin gwamnatin kasar Guinea sun dauki matakai, na gani duk inda aka samu bullar wannan cutar, ko gida ko anguwa. Sannan duk wadanda ke ma’amala da wanda ya kamu da wannan cuta, ana kula dasu har sai an basu kwanaki ashirin da daya an tabbatar basu kamu da wannan cutar ba, idan kuma sun kamu sai a kaisu asibiti a killace su.

Ya kara da cewa a Najeriya an fara rade-raden amma an fito an duba kuma an bada sanarwa cewa ba zazzabin ebola bane.
XS
SM
MD
LG