Accessibility links

Rashin biyan kudaden alwus-alwus ya jawo yajin aikin likitoci a janhuriyar Nijar.

Jami'an kiwon lafiya a jamhuriyar Nijer sun tsunduma cikin wani yajin aiki a matsayin kashedi har na kwanakki biyu a fadin kasar Nijer.

Wannan yajin aikin na neman hakki ne da suka ce gwamnatin kasar ta taushe masu dangane da wasu kudaden alawus-alawus din da ya kamata a biya su.

Kungiyoyin sunce idan har bukatar su bata biya ba, to yajin aikin zai ci gaba face sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi.

Likitocin na kuma kokawa da rashin ingantaccen kulawa a fannin kiwon lafiya duk da alkawarin da gwamnati ta sha yi akai batare da biyan bukata ba.

Duk kokarin da muka yi domin jin ta baki bangaren mahukunta ko kuma ofishin kiyon lafiya abun ya ci tura.
XS
SM
MD
LG