Amurka Da Afghanistan Sun Kashe Fararen Hula Fiye Da Taliban

Amurka da dakarun sojin gwamnatin Afghanistan sun kashe fararen hula fiye da kungiyar ‘yan Taliban da 'yan ta'adda, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A cikin wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya laraba ta ce, a farkon watanni uku na shekarar 2019, dakarun gwamnati suka kashe mutane 305 da kuma raunata 303, yayin da kungiyoyin 'yan tawaye suka kashe fararen hula 227 sannan suka raunata 736.

Mata da yara sun kasance rabin wadanda aka raunata ko aka kashe daga duk wani mummunan aiki, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Duk da haka dai, ya kasance watannin farkon shekara da ba a sami yawan asarar rayuka ba tunshekarar 2013.

Majalisar Dinkin Duniya ta danganta raguwar asarar rayukan da raguwar hare haren kunar bakin wake da fa kasar dake fama da tashin hankalai.