Amurka Da Canada Da Mexico Zasu Hada Gwiwa Su Shirya Gasar Kofin Duniya a 2026

FIFA Gianni Infantino

Kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa ta bada izinin daukar bakwancin gasar cin kofin duniya a shekarar 2026 ga Canada da Mexico da kuma Amurka su yi hadin gwiwa wurin shirya gasar.

Kasashe mambobin kungiyar kwallon kafa ta FIFA sun kada kuru'a inda masu ra'ayin kasashe ukun su dauki nauyin shirya gasar hadin gwiwa suka samu kuri'u 134 a kan kuru'u 65 na wadanda basu ra'ayin hakan, yayin da Morocco ta zo ta biyu bayan kasashen uku.

A gobe Alhamis ne ake fara gasar cin kofin wannan shekarar 2018, inda Saudi Arabia zata raba rana da kasar Rasha mai masaukin baki.

Za a gudanar da kasar ta shekarar 2022 ne a Qatar.