Mutanen da aka dawo da su daga Hadaddiyar Daular Larabawan sun hada mata 90 da maza 310.
Kakakin ma'aikatar wajen Amurka Mathew Miller, ya ce Lokaci yayi da ya kamata a kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bayan da sojojin Isra’ila suka gano gawarwakin wasu mutane 6 cikin wadanda ake garkuwa da su a Gaza a karshen mako.
Tsohon shugaba Trump, kuma dan takarar jami’iyar Republican a zaben 5 ga watan Nuwamban 2024, ya ajiye damarsa ta bayyana a gaban kotu, kana maimakon haka ya umarci lauyoyin sa su shigar da karar a madadin sa.
Hukumar da ke kula da gasa da kare muradun masu amfani kaya ta tarayya (FCCPC), ta ba da wa’adin wata guda ga ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a kasuwannin da ke kara kazamin riba kan kaya da su rage tsadar farashin kayayyakin na su ko doka ta yi aiki kan su.
Alkalumman sun nuna cewa s mutane 170 ne suka mutu, sannan ambaliyar ta raba wasu dubu 2,005 da muhallansu a jihohi 28 cikin jihohi 36 na kasar.
Majalisar dokokin Najeriya ta bayar da umarnin janye kudirin dokar da ta yi niyyar dakatar da abin da ta kira ayyukan zagon kasa a kasar.
'Yan tawayen kasar Kamaru sun sake shiga gallaza ma mutanen kasar a cewa hukumomi. Tuni dai mutane su ka shiga gudu daga wuraren da 'yan tawayen ke tsananta ma mutane
Har yanzu ba a tantance yawan gawarwakin mutanen da ke karkashin tarkacen shara a birnin Kampala na Uganda ba.
A ci gaba da gano abubuwan al'ajibi da masu ilimin kimiyya ke yi, sun gano cewa ga dukkan alamu akwai dinbin ruwa karkashin duniyar Mars.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce shugaba Tinubu yana kaunar Arewa da al'ummarta kuma dalili kenan da yasa ya bada kashi 62 cikin 100 na majalisar zartarwar sa ga 'yan arewa. Abin da ya rage shine Arewa ta hada kai domin samun ayyukan ci gaba daga wannan gwamnati.
Kasuwannin hannayen jari a fadin duniya na tangal tangal, yayin da ake fargabar tsunduma cikin matsalar tsananin tsadar kaya musamman ma a manyan kasashe irin Amurka da Japan da sauransu
Domin Kari