Amurka Na Bikin Zagayowar Samun 'Yancin Kai

Amurka tana bukin zagayowar ranar samun yancin kai a yau Laraba.

Amurkawa na bukin cika shekaru 242 da samun yancin daga Birtaniya ne ta hanyar gudanar da liyafar zuwa wani fili ko gandu ayi gashe-gashe a ci abinci tare da ake cewa picnic da turanci da gudanar da fareti da kuma shirya wasan wuta.

Shugaban Amurka Dnald Trump da uwargidansa sun shiryawa iyalan sojoji liyafa a fadarsa ta White House.

Bukukuwan ranar hudu ga wata Yulin zai hada ne da abin da aka saba yi bisa al’ada karanta ayyanar samun yanci a matakalar cibiyar adana kayan tarihi ta kasa a nan birnin Washington. A cikin ginin kuma, za a baje muhimman takardu tare da kundin tsarin mulki kasar da kuma dokokin yanci domin jama’a su duba.

Jim kadan bayan jawabin ayyana samun yancin, dubban mutane zasu yi fareti a gaban ginin a kan titin Constitution kuma faretin zai mike zuwa yammacin ginin kuma yake tsakanin fadar White House da dandalin tunawa da shugaban Amurka na farko George Washington.