Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yiwa Amurka Kashedi Akan Kara Haraji


Sakataren Cinikayya na Amurka Wilbur Ross
Sakataren Cinikayya na Amurka Wilbur Ross

Kungiyar tarayyar turai ta ja kunne Amurka akan shirin kara kashi 20 na haraji akan motocin da ake kerawa a Turai cewa tattalin arzikin Amurka ne zai komade

Kungiyar kasashen Turai tayi wa Amurka kashedin cewa shirin da shugaba Donald Trump yake yi na kara aza harajin kashi ashirin daga cikin dari akan motocin da ake kerawa a turai zai yi mugun kassara tattalin arzikin Amurka, kuma zai iya janyo suma kasashen turai su maida martanin sakawa kayayyakin da Amurka take sayarwa kasashen su haraji akan kimamin kayayyakin dala biliyan maitan da casa’in da hudu.

A wata wasika mai shafi goma data aikawa ma’aikatar cinnikayya a ranar Juma’ar data shige, kungiyar kasashen turai tace babu hujjar sakawa motoci da kayayyakin motocin da ake kerawa a turai haraji, kuma daukan wannan mataki na iya zama kuskuren tattalin arziki sosai.

Sakataren harkokin cinnikayya na Amurka Wilbur Ross jiya Litinin ya fadawa gidan talibijin na CNBC cewa za’a yi garaje ga dami idan aka ce shugaba Trump zai aiwatar da shirin kara kudin harajin.

A halin da ake ciki kuma shugaba Trump ya caccaki kungiyar harkokin cinnikayar kasa da kasa da ake cewa WTO a takaice, cewa ta dade tana yiwa Amurka rashin adalci.

Yace idan kungiyar bata yiwa Amurka adalcin daya kamata ba, to zasu dauki wani mataki, to amma kuma bai bada wani karin haske akan matakin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG