Amurka Ta Gargadi Iran Kan Gwajin Makami Mai Linzami

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Alhamis cewa, an yiwa Iran kashedi a hukumance a kan gwajin makamai masu linzamin da ta yi cewa, za a iya daukar kowanne irin mataki akan Tehran.

A cikin sakonnin da ya tura ta twitter, Trump ya kuma ci gaba da kushewa yarjejeniyar da Amurka da manyan kasashen duniya biyar suka cimma na dakatar da ayyukan nukiliyan Iran, ita kuma a saka mata da sassauta takunkuman da aka kakaba mata.

Ya ce kamata ya yi Iran ta gode da cimma wannan yarjejeniyar, ya ce kasar ta na shirin durkushewa kafin a sakar mata biliyoyin daloli.

Daga baya da yake amsa tambayar wani dan jarida da ya tambaya ko ta na yiwuwa a dauki matakin soja, Trump ya ce ana iya daukar kowanne irin mataki.

Yarjejeniyar da aka cimma ta bukaci Iran ta rage ayyukanta na nukiliya ta maida cibiyoyin aikin nukiliyarta na gudanar da wadansu ayyukan daban.