Amurka Tace Baza'a Lamunta Da Irin Zuba Jini Da Ake Yi A Libya Ba.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta kushewa tashin hankalin da ake yi a Libya ta kuma ce ba za a lamunci zubda jinin da ake yi ba.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta kushewa tashin hankalin da ake yi a Libya ta kuma ce ba za a lamunci zubda jinin da ake yi ba.

A cikin jawabin da tayi a Washington jiya talata, Clinton tace Amurka tana sa ido kan abinda ke faruwa a Libya kuma hankalinta ya tashi ainun. Bisa ga cewarta, alhakin yana kan gamnatin Libya, kuma tilas ne ta dauki matakin kawo karshen tashin hankalin da kuma mutunta ‘yancin dukkan mutanen kasar.

Clinton tace Amurka ta damu ainun dangane da tashin hankalin da ake yi a Yemen da kuma sauran kasashen gabas ta tsakiya. Ta kuma yi kira ga gwamnatocin yankin su kai zuciya nesa su kuma mutunta ‘yancin mutanensu. Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniy ya kushe da kakkausar murya yadda ake amfani da karfin soja wajen shawo kan masu zanga zanga a kasar Libya tare da kira da a kawo karshen tashin hankalin ba tare da bata lokaci ba.

A cikin sanarwar da jakadiyar kasar Brazil Maria Liza Ribeiro Viotti wacce take shugabancin da ake karba karba a kwamitin wannan watan, tace kwamitin sulhun mai membobi 15, ya yi kira da a kawo karshen tashin hankalin ba tare da bata lokaci ba.

Membobin kwamitin sulhu sun bayyana matukar damuwa dangane da lamarin na Libya. Sun kushewa amfani da karfi kan farin kaya da murkushe masu zanga zangar ruwan sanyi, suka kuma bayyana takaici ainun dangane da mutuwar daruruwan farin kaya. Tare da yin kira da a dauki matakin biyan bukatun al’ummar da suka hada da tattaunawa ta kasa. Mataimakin jakaden Libya a Majalisar DinkinDuniya Ibrahim Dabbashi, yace sanarwar majalisar bata da karfin kirki, sai dai mataki ne mai kyau na kawo karshen zubda jinni. Manzon wanda ya yi kira da a kauda gwamnatin Mr. Gadhafi tare da goyon bayan kusan dukan jami’an jakadancin Libya, yace rundunar soji ta fara kaiwa farin kaya hari.

Yana da abokanshi a rundunar soja kuma sun tara dakaru suna kaiwa mutane hari a dukkan biranen dake yammacin Libya. Babu shakka mutanen basu da makamai. Kuma ina tsammani an fara kisan kare dangi a Libya, ina tsammani jawabin Gadhafi alama ce ga abokan hada bakinsa su fara kisan kare dangi kan mutanen kasar.

Wannan na faruwa ne yayinda kungiyar hadin kan larabawa ta dakatar da Libya daga halartar tarukan kungiyar sakamakon rahotannin dake nuni da cewa, jami’an tsaron kasar suna kara amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga zangar kin jinin gwamnati.

Shugaban kungiyar hadin kan larabawa Amr Moussa ya jagoranci wani taron gaggawa jiya Talata domin tattaunawa a kan lamarin Libya. Ya bayyana a birnin alkahira cewa, tilas ne a kawo karshen karshen murkushe masu zanga zangar da ake yi.