Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gadhafi Ya karyata Cewa Yana Neman Mafaka A Venezuela


Wani dan kasar Libya yake dauke da bangaren jikin wani a asibitin Jalala dake kasar.

Shugaban Libya Moammar Gadhafi da ya kankare yana daukar matakan murkushe zanga zangar dake kara bazuwa a duk fadin Libya,yayinda sojoji,’yansanda da jami’an difilomasiyya suke barin wuraren ayyukansu

Shugaban Libya Moammar Gadhafi da ya kankare yana daukar matakan murkushe zanga zangar dake kara bazuwa a duk fadin Libya,yayinda sojoji,’yansanda da jami’an difilomasiyya suke barin wuraren ayyukansu,kuma wani bangaren kasar aka ce ya fada hanun masu zanga zanga.

An nuna shugaban na Libya a tashar talabijin ta kasar na wani dan gajeren lokaci cikin wata laima ya fidda kai daga cikin wata mota yana cewa har yanzu yana Tripoli ba Venezuela ba. Rahotannin farko da aka samu sunce Gadhafi yana Venezuela inda yake neman mafaka.

Rahotanni daga Tripoli babban birnin kasar sunce jiragen yaki da masu saukar ungulu sun kai farmaki a wasu sassan birnin jiya litinin,amma dan shugaba Gaddafi,Saif al-islam Gaddafi yace jiragen sun kai hari ne kan wurin adana albarusai.Shaidu a Tripoli sun bada rahotanni daban daban na ganin sojojin haya ‘yan Afirka sun bude wuta kan masu zanga zanga. Mutum biyu mazauna birnin, sun ce sun ga sojojin haya ‘yan Afirka suna sauka daga wani jirgin soja mai daukar kaya a wata tashar jiragen soja da bashi da nisa da babban birnin kasar.

Mazauna birnin sunce gungun magoya bayan Gaddafi sun kwace dandali da ake kira Green Sq, bayanda mayakan sakai suka bude wuta kan masu zanga zanga nuna kin jinin gwamnati. Majalisar dokokin kasar da gine ginen tashar talabijin din Libya biyu, suna cikin wurare da masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati suka bankawa wuta yayinda suke fafatawa da jami’an tsaro, da magoya bayan gwamnati.

Kungiyar kare hakkkin bil’adam ta Human Rights watch ta ce ta gaskanta an kashe mutane 233 a boren na kwanaki biyar,galibi a larduna dake gabashin kasar,d a aka bada labarin suna hanun masu hamayya da gwamnatin Gaddafi.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa mai cibiya a Paris ta fada jiya litinin cewa akalla biranen kasar tara ciki hard a bengazi,Sirte,da Misrata suna hanun ‘yan zanga zanga.Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da haka,kuma sadarwa da Libya daga waje tana kara wahala.

A wani lamari an sami rarrabuwar kawuna cikin gwamnatin Libyan,wasu manyan jami’an gwanati ciki har da ministan shari’a,da wakilan kasar a majalisar dinkin Duniya sun raba gari da Gadhafi.

Mukaddashin jakadan Libya a Majalisar Dinkin Duniya Ibrahim Dabbashi, ya yi kira ga shugaban dake tsaka mai wuya da ya yi murabus, kuma a gurfanaddashi kan laifuffukan yaki. Yana zargin gwamnatin da kaddamar da kisan kare dangi kan al’umar Libya.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG