Amurka Zata Kare Kanta Daga Barazanar Koriya Ta Arewa

Zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Amurka ta shaidawa jamia’an kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya jiya laraba, cewa a shirye take tayi anfani da karfin soja domin kare kanta daga barazanar kasar Koriya ta Arewa wadda ta kaddamar da gwajin makamin ta mai linzami.

sai dai kuma Amurkan tace zaifi kyau aga cewa an samu sulhu ta hanyar diflomasiyya da matakan tattalin arziki.

Harba makami mai linzami samfurin ICBM na farko da kasar Koriya ta Arewa tayi yaci karo da suka daga sassan duniya daban-daban, wanda kuma ya haifar da shigar ta cikin halin damuwa a fannin diflomasiyya.

Wadansu sassan kasashen arewacin Amurka anyi imanin cewa wannan makamin da kasar ta koriya ta Arewa ta sake harbawa a ranar talatar data wuce yana cikin sabbin rokokin ta data gwada ranar talata.