Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Nasarar Harba Makamin Da Zai Kai Amurka - Korea ta Arewa


Makami mai linzami (mai tafiyar dogon zango) da Korea ta arewa ta harba a baya-bayan nan yana tafiya a sama
Makami mai linzami (mai tafiyar dogon zango) da Korea ta arewa ta harba a baya-bayan nan yana tafiya a sama

Duk da kokarin da Amurka ke yi na ganin ta dakile ayyukan kera makaman nukiliya da kasar Korea ta arewa ke yi, hukumomin Pyngyong sun ce sun yi nasarar harba wani makami mai linzami da zai iya kai wa Amurka.

Korea ta Arewa ta ce ta samu nasarar gwajin wani makami mai linzami dake cin dogon zango, wani muhimmin ci gaba a kokarin kasar na habaka makaman nukiliyar da take yi duk da jan kunnen kasashen duniya.

Wannan makami mai linzami da aka harba daga wani filin jirgin saman dake kusa da bakin iyakar kasar da China a arewa maso gabas, ya fada a cikin yankin ruwan tekun Japan, ya kuma girgiza ‘yan siyasar Japan tare da tabbatar da cewa China ba za ta iya hana Korea ta arewan yin abinda take so ba.

Harba wannan makami mai linzamin da kasar ta ce zai iya kaiwa ga ko ina a duniya, zai kara matsin lambar da ake yi ma kasar China a kan ta kara daukar matakan takunkumi masu tsauri a kan Korea ta arewa.

Sai dai ba a san irin martanin da Korea ta arewan za ta maida ba.

A wajen wani taron ‘yan jarida a yau talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Geng Shuang, ya ce Beijing tana kokari babu-ji-babu-gani domin shawo kan kalubalen da ake fuskanta a yankin kasashen na Koriya.

Har ila yau ya ce China tana taka rawar da babu wanda zai iya maye gurbinta, yana mai kira ga dukkan sassan da su kai zuciya nesa domin warware wannan tankiya cikin sauri.

Shugaba Trump na Amurka yana kokarin ganin China ta kara matsin lamba a kan KTA, amma a karshen watan da ya shige, ya ce ko da yake yana yabawa da kokarin da shugaba Xi Jinping ke yi a kan Korea ta arewan, kokarin nasa bai haifar da abinda ake so.

A yau talata, firai ministan Japan, Shinzo Abe na ya ce wannan gwaji na baya-bayan nan ya nuna cewa irin barazanar da ake fuskanta daga Korea ta arewa ya karu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG