An Bayar Da Belin Ibrahim Magu

A Najeriya, bayan da aka yi ta kai ruwa rana tsakanin lauyoyin Ibrahim Magu da aka dakatar daga shugabancin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC), da kwamitin da ke binciken sa akan badakalar da ake zargin ya tafka da kuma hukumar ‘yan sanda da ke da alhakin bayar da shi beli, yanzu dai hukumar ‘yan sanda ta bayar da belin Ibrahim Magu amma ba a bayar da wasu bayanai ko sharudda da aka gindaya masa kafin a bada belin ba.

Wasu makusantansa sun tabbatar wa Muryar Amurka cewa yanzu haka Magu ya na gidansa bayan da aka bayar da belinsa.

Wani lauya mai zaman kansa, Barista Abdulhamid Mohammed, ya ce kwamitin na bincike ba wai kotu ba ce ta musamman ko wadda aka kafa mai zaman kanta, kawai bincike ya ke yi domin tabbatar da cewa wadannan laifuffukan da ake ganin an yi sun tabbata, dan haka a dokar Najeriya ba mai laifi ba ne har sai an kama shi da laifi.

Barista Abdulhamid ya kara da cewa ba a kama mutum da laifi don ana binciken sa har sai an tabbatar da laifin akansa kuma ko da an tabbatar kotu na iya bada belin sa bisa wasu dalilai.

Sai dai har yanzu hukumar ‘yan sanda ko shi Magu babu wanda ya bayyana sharudan belin na sa da aka bayar.

Saurari cikakken rahoton Umar Farouk Musa:

Your browser doesn’t support HTML5

An Bayar Da Belin Ibrahim Magu