An Bayyana Kudaden Hajji Na Bana Daga Najeriya

Masallaci Mai tsarki na Qaaba a Makkatul Mukarrama

Babbar kujera daga Arewa bana zata kama a kan kusan Naira dubu 751, matsakaiciya a kan kusan Naira dubu 673, karama kuma kimanin naira dubu 636.
Hukumar alhazai ta tarayyar Najeriya ta bayarda sanarwar yawan kudaden da mahajjata na bana masu tafiya ibada a Kasa mai Tsarki za su biya.

Bayanin da hukumar ta bayar ya nuna cewa a bana, babbar kujera daga Arewa zata kama a kan Naira dubu dari bakwai da hamsin, da dari tara da casa'in da shida (N750,996); matsakaiciyar kujera a kan Naira dubu dari shida da saba'in da biyu da dari tara da casa'in da shida (N672,996); sai kuma karamar kujera a kan naira dubu dari shida da talatin da shida da dari hudu da casa'in da shida (N636,496).

Daga yankin Kudancin Najeriya, kudaden da mahajjatan zasu biya a bana sune, babbar kujera Naira dubu dari bakwai da hamsin da takwas da dari uku da sittin da tara (N758,369); matsakaiciyar kujera Naira dubu dari shida da tamanin da dari hudu da sittin da tara (N680,469); sai kuma karamar kujera a kan Naira dubu dari shida da arba'in da uku da dari takwas da sittin da tara (N643,869).

Hukumar ta ce an samu kari fiye da shekarar da ta shige a saboda an samu karin kudaden gidajen saukar da mahajjatan a can Kasa Mai Tsarki.

Ga Nasiru Adamu el-Hikaya da cikakken bayanin yawan kudaden da kuma sanarwar da hukumar lahazan ta bayar.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bayyana Kudaden Kujerun Hajji Na Bana - 1:59