An Bukaci ECOWAS Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Akan Gwamnatin Guinea Bissau

President Guine-Bissau Jose Mario Vaz

Masu rajin kare demokradiyya sun gargadi mahalarta wannan taro su dauki matakin ba sani ba sabo.Yayinda shugabannin kasashen Afirka mambobin kungiyar ECOWAS ke shirin gudanar da taro a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, akan rikicin siyasar da ya barke a kasar Guinee Bissau,

Matakin da shugaba Mario Vaz ya dauka don rusa gwamnatin kasar tare da maye gurbinta da wata sabuwa, ya sa kungiyar Cedeao ta gargadi shugaban kasar ta Guinea Bissau ya canza ra’ayi ko kuma ya fuskanci fushinta.

Sai dai da alama wannan barazana ba ta yi tasiri ba,abinda ya sa shugabannin kasashen Afirka ta Yamma kiran wani taro a wannan juma’a a birnin Yamai.

Sai dai,ra’yoyin jama’a sun banbanta dangane da wannan dambarwa domin wasu ‘yan fafitika na ganin kungiyar ta ECOWAS na rufe ido akan wasu batutuwan da ya kamata ta tsawata.

A sanarwar da wani wakilin ECOWAS ya bayar dangane da lamarin, a birnin Bissau, kungiyar ta dibarwa ministocin sabuwar gwamnatin Faustino Imbali wa’adin awoyi 48 su yi murabus ko kuma su fuskanci hukunci.

A ranar 24 ga watan Novamba nan ne ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Guinee Bissau, to amma rashin daidaituwa a tsakanin shugaba Mario Vaz da Firai Minstansa ya sa shugaban rushe gwamnati a watan Oktoba.

Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci ECOWAS Ta Dauki Mataki Mai Tsauri Akan Gwmnatin Guinea Bissau