An Dauki Matakin Tabatar da Rigakafin Yara a Jamhuriyar Nijar

Ana digawa wata jaririya maganin rigakafi

Ganin irin yadda iyayen yara suke kin kawo yaran su zuwa asibiti domin yi masu rigakafi, likitoci a Maradi ta jamhuriyar Nijar sun dau wani sabon mataki na ganin ana yiwa yara rigakafi.
Ganin irin yadda iyayen yara suke kin kawo yaran su zuwa asibiti domin yi masu rigakafi, likitoci a Maradi ta jamhuriyar Nijar sun dau wani sabon mataki na ganin ana yiwa yara rigakafi.

Madam Uwaisu Aishatu ta bangaren yara a Maradi ta fadi cewa, suna bada rigakafi domin cututuka da dama saboda haka mata ya kamata su rika zuwa da yaransu domin awo da sauransu. Ta dai ce, sukan turo ma'aikatan kiwon lafiya zuwa gida gida domin bada rigakafi amma har yanzu akwai matsalar rashin zuwan awo a jihar.

Ta kara bayyana cewa matan karkara ke zuwa asibiti fiye da matan da ke birni. Tace, yawancin matan da suke samu ba matan Maradi bane.

Madam Aishatu ta kuma ce suna yin iyakan kokarin su domin wayar da kan mata a kan amfanin zuwa asibiti domin yin awo.

Your browser doesn’t support HTML5

Likitoci sun sake dabarar rigakafi a nijar - 2:31