Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cututukan Da Gurbacewar Muhalli Ke Haifarwa


Girke-girke

Gurbatar muhali baya ga barazana da yake yi wa al'uma, musaman a kasashe irin su Najeriya, wanda suka danganci kamfanoni game da hayakin mashin da ke fitowa yana bata yanayi, hakan na haifar da cututukan da dama da ke barazana da lafiyar al'uma.

Gurbatar muhali baya ga barazana da yake yi wa al'uma, musaman a kasashe irin su Najeriya, wanda suka danganci kamfanoni game da hayakin mashin da ke fitowa yana bata yanayi, hakan na haifar da cututukan da dama da ke barazana da lafiyar al'uma.

Baya ga hayakin kuma warin da kamfanonin ke janyowa al'umma su dai wadannan cututuka da gurbatar muhalli ke haddasa su sannu, a hankali su ke shiga cikin jkin mutum, su taru su kuma kawo ila ga lafiyarsa.

Wani likitan al'uma da ke asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dr Usman Bashir, yayi bayani akan ilolin muhali ga lafiyar bil'adama da irin cututukar da mutum ke iya dauka.

Dr Bashir yace, "Hayakin da suke tasowa na girke-girke, na janareto, na motoci, wanda suke gurbata muhali, sukan kawo cututuka dayawa, ko kuma su tsananta wasu cututuka, kamar cutar Asma."

Ya kuma ce, "Wadansu cututukan sukan shiga jini suyi illa."

Dr Bashir ya bukaci mutane su kare kansu daga shakan wadanan hayaki da kuma zuwan asibiti domin a duba lafiyar su da zarar sun fuskanci wani canji a lafiyar jikinsu.

Ga cikakken rahoton da Barak Bashir ta aiko.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG