Accessibility links

Za’a iya kare kai daga kamuwa da kashi talatin daga cikin dari na cutar kansa idan mutum yayi rayuwa kiyaye lafiya mai kyau in ji Ministan lafiya Mai girma Sherry Ayitey.

Za’a iya kare kai daga kamuwa da kashi talatin daga cikin dari na cutar kansa idan mutum yayi rayuwa kiyaye lafiya mai kyau in ji Ministan lafiya mai girma Sherry Ayitey. Yayinda take magana a lokacin kaddamar da ranar kansa ta duniya a Accra, Ayitey tace irin rayuwa kamarsu shan taba, shan giya da shafa maganin canza launin fatai, da kuma hadarorin gurbataccen yanayi kamar su shakar kazamar iska da kuma shakar iska mai guba suna kara hadarin cutar kansa.

Tace gwamnati na kokari sosai wajen kawarda da kuma kiyaye cutar kansa, wanda za’a iya gani ta wajen bullo da shirin kiyaye kansa na kasa wanda za’a gudanar a cikin shekaru biyar.

Ta kara da cewa Ghana tana da manyana cibiyoyin yaki da kansa guda biyu wadanda ke bude ga dukan jama’a wadanda kuma suke da kayayyakin aiki kamarsu kayan kona cutar kansar a asibitin koyarwa na Korle-Bu a Accra da kuma asibitin koyarwa na Komfo Anokye wanda yake a Kumasi, inda ake bada magungunan cutar kansa.

Direktan dake kula da fida na asibitin koyarwa na Korle-Bu, Prof. Joe Nat Clegg Lamptey, ya bayyana cewa mutuwar da ake samu daga cutar kansa tafi ta cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da kuma cutar tarin fuka.

Farfesa Lamptey, yace kiyasci ya nuna cewa kimanin matsalar kansa 2,260 aka samu cikin wannan shekarar kuma an sami mace mace na kansa kimanin 1,021.

Ya nuna cewa kudin yin maganin cutar da ta yi nisa yakan kai 40,000 na Ghana Cedis, ya kara da cewa gano cutar da kuma fara magani da wuri itace babbar shawara.
XS
SM
MD
LG