An Fara Jigilar Alhazan Jihar Kano

Alhazai

A Kano an tara maniyattan jihar a sansanin alhazai kafin su tashi zuwa Saudiya. Sun samu horaswa daga malamai tare da 'yan hukumar hisban jhar.

Maniyattan da aka zanta dasu suna begen zasu sauka a Makka ko Madina. Yanzu suna jira ayi masu binciken karshe ne kafin su tashi.

Ranar Talatar da ta gabata aka fara jigilar alhazan jihar Kano wadanda adadinsu ya kai dubu biyar da dari bakwai da takwas.

Alhaji Lamir Rabiu sakataren zartaswa na hukumar alhazan jihar yace kawo yanzu sun yi jirgi biyu da alhazan Kano kimanin dubu daya da ishirin. Kawo yanzu sun sami takardar shiga kasar Saudiya fiye da kashi casa'in cikin dari kuma suna sa ran zasu samu sauran. Dangane da canza kudin alhazan a bankuna yace basa samun cikkas.

Idan abubuwa sun tafi daidai cikin kwana goma zasu gama jigilar alhazan. Kamfanonin jirage uku ne zasu yi jigilar.

Dr Mansur Mudi Nagode shugaban jami'an tawagar da zasu kula da alhazan a kasa mai tsarki yace basu bari masu cuta dake da damuwa sun shige tantancewa da suka yi ba. Ma'ana duk wanda yake da wata damuwa an cireshi daga jerin wadanda zasu yi aikin hajjin bana. Wadanda suka cancanta aka bari suka tafi.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Jigilar Alhazan Jihar Kano - 2' 59"