Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Hukumar Alhazai Ya Saci Miliyan 30


Kaaba a Mecca.

Maniyyatan hamsin daga jihar Nejar, sun shiga halin rudani tare da rashin sanin makomansu game da sauke Farali a bana

A yayi da Maniyyata akin Hajjin bana daga Najeriya, hankalinsu ya fara kwantawa, a sakamakon fara jikilansu, a kashen makon nan da ya gabata.

Su kuwa wasu Maniyyatan su hamsin daga jihar Nejar, sun shiga halin rudani, tare da rashin sanin makomansu game da sauke Farali a bana.

Saboda kudin da suka biya fiye da Naira miliyan talatin, wani jami’in hukumar Alhazan jihar Nejar, Bala Barkuta, yayi sama da fadi dasu.

Koda yake bayyanai na nuni da cewa wannan jami’in a yanzu haka yana hannun hukomomin tsaro domin gudanar da bincike akansa.

Hukumar Alhazan jihar Nejar, ta bada tabbacin cewa Maniyyatan zasu samu zuwa sauke Farali abana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG