An Fara Neman Jirgin Malaysia a Karkashin Teku

​Ma’aikata a can-can kudancin tekun Indiya sun fara binciken karkashin ruwa suna neman na’u’rar daukar bayanan zirga-zargar jirgin Malaysian nan wanda ya bace, wanda batirinshi zai iya karewa a kwanaki masu zuwa.
Babban hafsin sojojin Saman kasar Australia mai ritaya, Marshal Angus Houston yau Juma’a yace wani jirgin ruwan mayakan Amurka ya dauki wani abu mai iya gano na’u’rar daukar bayan zirga-zirgar jirgin sama, kuma ya je can wani waje a cikin tekun kudancin Indiya din mai fadin kilomita 240 domin gani ko za’a ji alamar jirgin.

Jami’ai sun kiyasta cewa suna da nan zuwa ran Litinin kafin batiran na’urar bayanan su kare kaf.

Yau dai kwanaki 30 kennan tun bayan bacewar jirgin mai kirar Boeing, samfurin 777, wanda yake kan hanyarshi zuwa birnin Beijing, daga Kuala Lumpur. Kasashen duniya da yawa sun yi kokarin samo shi amma har yanzu shiru.