Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Lallai Bane a San Me Ya Samu Jirgin Malaysia - inji Jami'in Kasar


​Babban jami’in hukumar ‘yan sanda ta kasar Malaysia na fa gargadin cewa wata kila ba lallai bane jami’ai su gano abunda ya faru da jirgin Malaysia wanda ya bace mai lambar tafiya dari uku da saba’in.

Wadannan kalamai na yau Laraba sun zone kwanaki 25 bayan bacewar jirgin mai kirar Boeing samfurin 777, wanda yake hanyarshi zuwa birnin Beijing na kasar Chana, daga Kuwala Lumpur na Malaysia dauke da mutane 239.

Binciken kasa da kasa domin gano baraguzen jirgin a kudancin tekun Indiya ya ci tura, kuma ‘yan sanda Malaysia suma sun yi bincike amma basu samo komai ba.

Sfeto Janar Khalid Abubakar yace masu bincike na bukatar karin lokaci domin neman shaidu, kuma yayi gargadin cewa fa za’a iya daukar lokaci mai tsawon gaske ana wannan bincike.

Khalid ya kara da cewa ‘yansanda na cigaba da mayar da hankulansu akan yiwuwar an sace jirgin ne, ko akwai wata kumbiya-kumbiya, ko kuma akwai mai tabun hankali a cikin jirgin.

Yanzu dai, a cewar Khalid masu bincike sun tambayoyi ga mutane har sau 170, kuma yace za’a cigaba da yin tambayoyi.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG