An Hallaka Wasu 'Yan Bindiga A Misira

  • Ibrahim Garba

Wasu jojojin Misira na aikin tabbatar da tsaro

Jami’an tsaron Misra sun ce a jiya Asabar an kashe tare da raunata wasu mutane da dama da ake kyautata zaton mayakan Islama ne
Jami’an tsaron Misra sun ce a jiya Asabar an kashe tare da raunata wasu mutane da dama da ake kyautata zaton mayakan Islama ne a wani babban samamen da aka kai kan ‘yan bindiga a arewacin Sinai.

An yi amfani da tankokin yaki da jiragen yaki masu saukar ungula ke rufa wa baya, a samamen da aka kai kan mabuyar ‘yan bindiga da ke kewayen garin Sheihk Zuweid, da ke daura da kan iyakar Zirin Gazar Falasdinawa.

Jami’ai sun ce sun kama ‘yan bindiga da dama a yayin wannan samamen.

Mazauna wurin sun ce al’amarin na iya zama matakin soji mafi girma da aka taba gani cikin shekaru da dama. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce jami’an Misra sun rufe kan iyakar Gaza saboda wasu dalilai na tsaro.

Wasu kungiyoyin ‘yan bindiga masu alaka da al-Qa’ida sun zafafa hare-haren da su ke kai wa kan jami’an tsaron Misra a yankin na Sinai tun bayan da aka hambare Shugaba Mohammed Morsi a watan Yuli.