An Kaddamar Da Cibiyar Tattara Bayanan Sirri a Jihar Filato

Cibiyar Tattara Bayanan Sirri a Jihar Filato

Gamayyar hukumomin tsaro dake jihar Filato ta kaddamar da wata cibiyar tattara bayanan sirri cikin gaggawa don tsaron rayukan jama’a musamman lokacin bukukuwan Sallah.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP Mathias Terna, ya ce cibiyar ta kasance da muhimmanci saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta, musamman lokutan bukukuwan Sallah.

Limamin babban masallacin Jos, Sheik Muhammadu Lawal Adam, ya yi huduba ne kan zaman lafiya da hakin da ya rataya kan shugabanni.

Shima shugaban darikar ECWA ta kasa da kasa, Rabaran Stephen Panya-Baba ya ce kamata yayi hukumomi su sauya fasalin yadda suke gudanar da harkar tsaro.

An dai gudanar da bukukuwan Sallah lafiya a fadin jihar Filato.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaddamar Da Cibiyar Tattara Bayanan Sirri a Jihar Filato - 3'19"