An Kai Hari A Abala Jamhuriyar Nijer

Rahotanni daga garin Abala wanda yake da nisan kilomita 255 daga Birnin Yamai na cewa ana gab da shan ruwa a yammacin jiya Laraba wasu ‘Yan bindiga suka kai sumame, Inda aka kwashe kusan awanni biyu suna kafsa fada da jami’an tsaro.

Wani mazaunin garin na Abala yace Yan bindigar sunyi shigar burtune ta hanyar amfani da Kakin Sojojin Nijar ne da wasu motoci biyar na aikin soja da suka sata a wani harin da suka kai a kwanakin baya a garin Ayyiru.

Har izuwa yanzu babu masaniyar ko an kashe yan bindigar ko kuma jikkata wasu daga cikinsu, Yazuwa yanzu da muke hada wannan rahoto hukumomin Niger basu ce komai a kaiba.

Koda yake bayanai na nuna cewa ministan cikin gida Bazoun Muhammed ya isa garin na Abala a dazu da safe domin tantance abubuwan da suka wakana inda ya halarci Jana’izar jami’an tsaron da suka kwanta dama a harin na jiya.

Ga rahoton Sule Mumuni Barma daga jamhuriyar Niger.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Hari A Abala Jamhuriyar Nijer