An kai hari a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya dake Mali

Harin da aka kai Mali

Mayakan sa kai na kungiyar Islama dake da alaka da kungiyar al-Qaida ta kai hari a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya dake Kidal kasar Mali

A Mali ofishin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya yace an kashe sojojinta uku a wani hari da aka kai yau jumma’a kan wani sansanins dake Kidal a arewacin Mali.

Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mahamat Saleh Annadif, yace an jikkata wasu mutane 30 sakamakon harin da aka kia d a safiyar yau Jumma’a.

Wasu majiyoyi daga rundunar kiyaye zaman lafiyar da ake kira MINUSMA a takaice, yace mayakan sakai masu ikirairn Islama sune suka harba rokoki kan sansanin. Kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa yace sojojin da aka kashen ‘yan kasar Guniea.

A cikin sanarwa da aya bayar, shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya Annadif, ya bayyana bakinciki kan harin da ya kira “kiyayya da rashin tarbiya.”