Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mali: Wasu mahara sun kai hari kan sojojin kiyaye zaman lafiya


Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita

Wasu 'yanbindiga sun kai hari kan sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Mali. Sojojin Najeriya ne suka fi yawa a sansanin

Rahotanni daga Mali sun ce wasu mahara da ba'a san ko su wanene bane sun kai hari kan ofishin sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake Timbuktu.

Rahotannin suka ce an fara kai harin ne da sanyin safiyar jumma'an nan. Shaidun gani da ido suka ce sun ce sun akalla wata fashewa, sai kuma karar bindiga suka biyo baya kusa da ofishin sojojin kiyaye zaman lafiya da ake kira MINUSMA. Sojojin Najeriya ne suke sansanin.

Akwai rahotannin cewa akwai wadand harin ya rutsa da su, amma babu wani bayani daga bangaren hukuma, an ce ana ci gaba da gwabza fada.

Idan ba'a manta ba kwana kwanan nan wasu 'yan ta'ada dake da alaka da kungiyar Al-Qaida yankin Maghreb ta kai hari wani otel dake Bamako babban birnin kasar da yayi sanadiyar hasarar rayuka da yawa. Har yanzu kasar bata farfado daga mummunan harin ba sai kuma ga wannan.

Muna bin digdigi domin samun cikakken bayani idan akwai kana mu kawo maku.

Ga karin bayani.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Mali ya sanar cewa sojojin majalisar da na Mali sun kwato sansanin 'yansanda dake Timbuktu da maharan suka mamaye yau Juma'a. Mai magana da yawun majalisar Olivier Salgado yace yanzu an kawo karshen fada a sansanin amma ana cigaba da neman bakiyoyi ko bamabamai da 'yan ta'adan ka iya boyewa.

XS
SM
MD
LG