An Kai Hari Kan Kakakin Majalisar Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Kakakin majlisar dokokin jihar Taraba ya tsallake rijiya da baya sanadiyar wani hari da aka kai masa.
An kai ma kakakin majalisar dokokin jihar Taraba Mr. Haruna Tsokwa hari a kauyen Bade dake jihar Kaduna tsakanin Jos da Abuja.

Harin ya zo kwana biyu bayan da kakakin ya shaidawa kotun da gwamna Danbaba Suntai ya shigar da kara cewa wasikar da aka ce gwamnan ya rubuta wa majalisar na cewa ya dawo daga jinya wasika ce ta bogi.

Maharan sun kai harin ne yayin da yake kan hanyarsa daga Abuja zuwa Jos. Kakakin na dawowa ne daga taron 'yan majalisun jihohi da suka yi a Obudu jihar Cross Rivers. Kodayake Mr. Haruna Tsokwa ya tsallake rijiya da baya to amma an harbi daya daga cikin 'yansandan dake tare da shi. Hadimin kakakin ta fuskar yada labarai Tanko Kaura ya ce kakakin na cikin koshin lafiya yayin da aka kwantar da dansandan a asibiti.

Tun dawowar gwamna Danbaba Suntai jihar Taraba ta samu kanta a wani dambarwar siyasa. To sai dai mukaddashin gwamnan Alhaji Garba Umar ya cigaba da kiran 'yan jihar su sani cewa shi ba wata gwamnati daban ya ke yi ba. Yana cigaba ne da aikin mai gidansa gwamna Suntai. Don haka a yi masa fatan alheri domin jihar ta cigaba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kai Hari Kan Kakakin Majalisar Dokokin Taraba - 2:30