Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shari'ar Danbaba Suntai Ta Dauki Wani Sabon Salo


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai
Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

An cigaba da sauraron karar da Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai ya shigar, inda yake kalubalantar matakin da ‘yan Majalisar Dokokin jihar suka dauka na cewa ya koma ya cigaba da yin jinya, shiko mataimakinsa Alhaji Garba Umar ya cigaba da riko a matsyin mukaddashi.

An yi ta tafka dogon turanci a kotun, tsakanin Lauyoyin Gwamnan, da na bangaren da na bangaren ‘yan majalisar da suka nace cewar kotun daukaka kara, ita ce take da hurumin fassara wannan takaddama.

Bayan wannan doguwar Muhawara, alkalin kotun Justice Ali Ibrahim Andaya Tsoho ya dage sauraron shari’ar, har zuwa ranar 30 ga wannan wata na Satumba domin cigaba da sauraron shari’ar.

SAN Yusuf Ali wanda yana daga cikin lauyoyin dake kara ‘yan majalisar, yayi bayanin ko meyasa lauyoyin suke bukatar zuwa kotun daukaka karar.

“Mu matsayin mu shine, batun da ake magana akai, sabon abu ne a dokokin kasar nan, don haka ne yakamata a mika batun ga kotun daukaka kara, wato Court of Appeal, domin jin nata ba’ahasin, “ a cewar SAN Yusuf Ali. “Kuma muna kyautata zaton samun nasara a wannan shari’a.”

Yanzu dai hankulan manazarta harkar shari’a ya koma ga dambarwar siyasar jihar Taraba, kuma lokaci ne ke tabbatar da abunda ka iya faruwa a lokacin da Alhaji Garba ke cigaba da jan ragamar jihar tare da kwamishinonin da suka ki ballewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG