Ana Tsare Da 'Yan Majalisar Dokokin Zamfara Bisa Umurnin Gwamna Yari

Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya

Yayin da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara yake musanta tsare 'yan majalisar, wani dan majalisa mai suna Umaru Mu'azu yace dukkan shugabannin majalisar su na hannun hukumar tsaro ta DSS

'Yan majalisar dokokin Jihar Zamfara sun yi kukar cewa an kama shugabanninsu, kuma a yanzu haka su na tsare a hannun hukumar tsaron cikin gida ta DSS bisa umurnin gwamna Abdul'aziz Yari.

'Yan majalisar suka ce an tsare shugabannin nasu ne biusa fargabar cewa su na shirin tsige gwamna Yari a saboda salon mulkinsa da kuma mawuyacin halin da jihar take ciki.

Kwamishinan yada labarai na Jihar Zamfara, Umaru Bukkuyum, ya musanta cewa ana tsare da 'yan majalisar, yana mai fadin cewa an gayyace su ne zuwa Abuja domin tattaunawar yadda za a yi sulhun sabanin dake tsakaninsu da bangaren gwamnan jihar.

Sai daiu kuma wani dan majalisa mai suna Umaru Mu'azu yace mutum daya ne tak daga cikin shugabannin majalisar dokokin ta Jihar Zamfara wanda ba ya hannun hukumar DSS a yanzu haka.

Rahotanni daga Gusau, hedkwatar jihar ta Zamfara, sun ce da yawa daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar sun gudu daga cikin jihar a saboda su na tsoron za a kama su a garkame.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya aiko mana...

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama An Daure 'Yan Majalisar Dokokin Zamfara Bisa Umurnin Gwamna Yari - 2'58"