Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Lallai Ne Cin Kitse Ya Zamo Mai Lahani Ga Lafiya Ba, Amma...


Sabon nazari ya nuna cewa cin kitse a wani bangare na irin abincin da kasashen yankin tekun Bahar Rum suka saba ci, ba zai yi illa ga jiki ba

Nazari ya nuna cewa cin kitse ba lallai ne yayi illa ga lafiyar mutum ba idan ya kasance ya fito ne daga wasu nau'o'in abinci, kuma tare da cin wasu kayan abinci irin wadanda aka saba ci a wani yanki na duniya

Wani sabon nazari na masana ya nuna cewa cin kitse, ko yana da yawa, ba lallai ne yayi illa ga lafiyar mutum ba.

Amma kafin mai karatu ya ruga kasuwa ya sayo nama mai kitse, ko ma kitsen kansa, masana sun ce wannan kitse da suke magana, tilas ne ya kasance wani bangare na irin nau'in abincin da aka saba ci a kasashen da suke yankin tekun Bahar Rum, abincin da ya kunshi 'ya'yan itatuwa, da ganyayyaki, da kifi, sannan bai cika kunsar nama ko madara ba. Irin wannan abinci, na kyale mutum ya ci kitse sosai, muddin dai kitsen wanda ya fito ne daga man zaitun, ko man 'ya'yan itatuwa, ko daga kwai ko kuma kitsen kifi.

A bayan cewa cin kitse mai yawa ta wannan hanya ba zai yi illa ga lafiya ba, binciken ya nuna cewa hakan ma yana iya rage kasadar kamuwa da wani ciwon zuciya, ko sankarar nono da mata ke fuskanta ko kuma ciwon sukari, in ji babbar mai binciken, Dr. Hanna Bloomfield.

Cibiyar Rigakafi da Yaki da Cututtuka ta Amurka, ta ce ciwon zuciya shine babban abinda ya fi kashe Amurkawa wadanda suka balaga. Cutar sankara kuwa ita ce ta biyu.

Dr. Bloomfield ta ce cin nau'in abinci irin na kasashen yankin tekun Bahar Rum zai taimaka wajen yakar cutar sankara ta hanyar rage yawan mutuwa daga cutar tare da rage kasadar kamuwa da cutar sankarar dubura da ta huhu.

An wallafa sakamakon wannan binciken ne a cikin mujallar nan mai suna "Annals of Internal Medicine."

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG