An Kama Shugaban Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi A Misira

Magoya bayan tsohon shugaban kasar Misira Mohamed Morsi

Hukumomin kasar Misira sun kama shugaban kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Mohammed Badie,a ci gaba da kai farmaki kan kungiyar bayan hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi.
Hukumomin kasar Misira sun kama shugaban kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi Mohammed Badie, a ci gaba da kai farmaki kan kungiyar bayan hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi.

An kama Badie dan shekaru 70 da haihuwa ne jiya talata da safe, a wata unguwa dake gabashin birnin Alkahira inda masu zanga zanga suka shafe makonni suna gamgamin yiwa gwamnatin rikon kwarya bore.

Ana kyautata zaton gurfanar da Badie gaban kulliya ranar 25 ga wannan watan na Agusta tare da wadansu shugabannin kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi. Hukumomi suna zarginsu da haddasa tashin hankalin da aka yi asarar rayuka, a kofar shelkwatar kungiyar cikin watan Yuni, ‘yan kwanaki kafin hambare gwamnatin Mr. Morsi.

Adadin wadanda suka mutu a tashin hankali a duk fadin kasar Misira tunda aka dauki wannan matakin ranar uku ga watan Yuli ya kai dubu daya. Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi tace adadin ya haura haka.

Wadansu mutane da ake kyautata zaton mayakan kishin Islama ne sun yi kwantan bauna suka kashe yan sanda 24 jiya Litinin da asuba a yankin Sinai.

‘Yan sa’oi kafin kwantan baunan jiya Litinin, ‘yan sanda suka kashe fursunoni ‘yan kishin Islama 36 a kusa da birnin Alkahira, wadanda aka yi zargin cewa, sun yi kokarin tserewa daga gidan yarin. Jami’an kasar Misira sun ce fursunonin sun mutu ne ta dalilin shakar barkonon tsohuwa.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tayi Allah wadai da tashin hankalin da ake yi a Misira amma ta bayyana shakkun dalilin mutuwar fursunonin. Kakakin ma’aikatar Jen Psaki ta kuma ce, Amurka ta hakikanta cewa, tilas ne dukan bangarorin su hada hannu wajen ganin ci gaban kasar Misira.