Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Haske Kan Rikicin Kasar Masar


Dan Misira dauke da akwatin gawa
Dan Misira dauke da akwatin gawa

Akwai karin haske kan rikicin kasar Masar yayin da ake tunani ko haka za'a cigaba da kashe mutane a kasar.

Rikicin kasar Masar kamar ba zai kare ba nan da 'yan lokaci domin jajewa da sojoji da 'yan'uwa Musulmai suka yi domin a jawabin Janaral Sisi ya ce sojoji a shirye suke su cigaba da yin anfani da karfi a kan wai suna yaki da ta'adanci ne.

Abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da masanin tarihi kuma mazaunin birin Alkahira. Kamar yadda ya fada al'ummar kasar tana kokarin hambarar da gwamnatin soja ta yin anfani da daukan matakan dabarun gargajiya yadda ba za'a rubar da jini ba kamar yadda shi Janaral Sisi ya ke son cigaba da yi. Ya ce suna da hanyoyinsu na gargajiya da suke anfani dasu wurin hambarar da duk wadanda suka yi masu milkin mallaka shekaru dubbai da suka gabata.

Wadannan tsare-tsaren na gargajiya sun hada da hadin kai, su ki bude kantuna kuma masu arziki su janye kudadensu daga bankuna domin su hana gwamnati anfani da arzikinsu. Su na iya kin zuwa ofisoshi. Suna iya kin bude duk wasu ma'aikatu. Duk wasu ayyukoki da suka shafi cingaban kasa zasu tsayar dasu sai dai abun da ya shafi jinkai kamar asibitoci da magunguna.

Dangane da yadda basu yi anfani da wadannan dabaru ba tun can farko suka bari ana yi masu kisan kiyashi sai ya ce hakan ta faru ne domin Janaral Sisi ya raba kawunansu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG