An Kashe Wani Sojan Amurka Na Musamman A Somaliya

Sojojin Somaliya a wani wuri da aka tada bom

An kashe wani sojan amurka na musamman, yayinda aka kuma jiwa wadansu hudu rauni lokacin da kungiyar da ake alakantawa da al-qaida ta kai hari jiya Jumma’a a wani wuri da ake gina karamin sansanin soji a kudu maso yammacin kasar Somalia.

An kai harin jiya jumma’a a wurin dake tazarar kilomita hamsin da birnin Kismayo ne yayinda dakarun Amurka ke taimakawa takwarorinsu na kasashen Somalia da Kenya gina karamin sansani, daga cikin ayyukan da rundunar sojin ke gudanarwa na kakkabe mayaka da kungiyar ta’ddanci ta al-Shabab daga yankin, bisa ga cewar jami’an rundunar sojin Amurka.

Shaidu sun ce an kai harin ne kusa da garin Sangumi, lokacin da dakarun Amurka da Somaliya da kuma Kenya suke gina ramukan shingen kariya suna kuma kakkafa wadansu hanyoyin kariya.

Suka ce mayakan sun fara da jefa nakiyoyi kafin suka bude wuta kan dakarun.

An tura jirgin helicopta domin daukar wadanda suka ji rauni.