An Kashe Wasu Palasdinawa Biyu Lokacin Zanga-zanga

An kashe wasu Palasdinawa biyu a wata arangama da tsakaninsu da dakarun Isra’ila, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin Palasdinu, yayin da ake ci gaba da yin zanga-zanga kan shawarar shugaban Amurka Donald Trump na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Sabon tashin hankalin dai ya barke ne kwana guda bayan da Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya yayi watsi da shawarar da Amurka ta yanke.

Ma’aikatar Lafiyar da kungiyar Hamas ke gudanar da ita, ta ce an kashe yaran masu shekara 24 da 29 da haihuwa ta hanyar harbi yayin arangama akan iyakar Gaza da Isra’ila.

An kiyasta kimanin Palasdinawa 2,000 suka fito zanga-zangar ta jiya a Gaza, Juma’a ta uku kenan tun da Trump ya sanar da cewa Amurka zata mayar da ofishin jakadancinta dake Isra’ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

Isra’ila na daukar ilahirin birnin Kudus a matsayin babban birninta na har abada, yayin da kuma Palasdinawa ke son gabashin birnin Kudus ya zama babban birnin kasarsu da za a kafa nan gaba, sannan suka ce Amurka ta daina zama wata abar dogaro game da batun samar da zaman lafiya.

Shawarar da Trump ya yanke ta harzuka dubban Palasdinawa har suka hau kan tituna suna zanga-zanga, kuma su kayi arangama da sojojin Isr’aila.