Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mota Makare Da Bama-Bamai Ta Kashe Mutane A Afghanistan


Jami'an tsaro a inda abin ya faru.
Jami'an tsaro a inda abin ya faru.

Wata mota mai cike da nakiyoyi ta kutsa cikin wani chaji ofis a wani gari a Afghanistan, daga bisani kuma matukin ya tada nakiyoyi, abinda yai sanadiyar rasa rayuka da kuma raunana mutane da dama.

Jami'an Afghanistan sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a yau Juma'a yayi sanadiyyar mutuwar a kalla 'yan sanda shida da kuma raunana mutane 10 ciki har da Kwamandan yanki a lardin Kandahar da ke kudancin kasar.

Dan kunar bakin waken ya kutsa ne cikin wani chaji ofis da ke gundumar Maiwand da wata mota irin ta soja da ake kira Humvee, wadda aka makare ta da nakiya.

Kwamandan 'yan sanda na shiyyar mai suna Sultan Muhammad ya shaidawa muryar Amurka cewa, tashin bam din yayi sanadiyyar tarwatsa ofishin 'yan sandan da kuma gidanjen mutanen da ke makwabtaka da su.

Ya kara da cewa ‘yan sandan da aka girke a mashigar farko, sun yi kokarin tsayar da motar da ta yo dakon bama-baman da nauyinsu ya kai kimanin kilo dubu uku ta hanyar budewa motar wuta, amman direban ya samu nasarar kaiwa ga kofa ta biyu kafin ya tayar da nakiyoyin.

Tuni dai ‘yan Taliban suka dauki alhakin kai wannan hari.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG