An Kashe 'Yan Boko Haram 40, Tare Da Kwato Makamai

Dakarun kungiyar kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi na Rundunar "Operation 'Yancin Tafki" sun ragargaza mayakan Boko Haram, inda suka kashe mayaka 40.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Kanar Timothy Antiga, ya sanyawa hanu, tace an fafata ne a yankin Login Komadogou, dake kan iyakar Najeriya da Nijar, ta bangaren Guedkerou kimanin kilomita talatin daga jihar Difa a bangaren jamhuriyar Nijar.

Sojojin kasashen yankin tafkin Tchadin kamar yadda sanarwar ta nuna, sunyi likimo ne har saida mayakan na Boko Haram suka tunkaro, inda sojojin suka afka musu. Nan take kuma suka lashe guda ashirin da bakwai, sannan an kame manyan bindigogi da harsasai masu yawan gaske.

Rundunar kasashen yankin tafkin Tchadin, sun kai wani mummunan hari ga mayakan na Boko Haram a yankin Abadam na Mallamfatori, cikin Najeriya.

Sojojin sun kashe 'yan Boko Haram 13 Tare da kwato manyan bindigogi 20 da wasu bindigogin harbo jiragen sama guda 5 da akwatinan harsasai.

Bugu da kari, sojojin sun kuma rugurguza motocin yakin Boko Haram guda 5, kana sun kwato karin wasu motocin yaki guda uku da bindigogi kirar Machine Gun 3, da gurneti guda 3, sannan an cafke wani dan bindigar daya a raye.

Baki daya kimanin mayakan Boko Haram 40 kenan dakarun suka kashe a wannan sabon farmakin mai take Operation Yankin Tafki.

Ga rahoton wakilin sashen Haussa na muryar Amurka Hassan Maina kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kashe 'Yan Boko Haram 40, Tare Da Kwato Makamai 2'30"